Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillacinTurk press ya bayar da rahoon cewa, Ahmad Qurnaz wani kwararre kan gyaran kayan tarihi yana gudanar ad aikin gyaran dadaden kur’ani a Turkiya.
Bisa ga dalilai na tarihi da aka dogara da su, kur’ani yana da kimanin shekar 455 a halin yanzu da rubutawa, wanda wata mata Disaz matar sarki Mahmud na biyu an Daular Usmaniyya ta bayar da shi kyauta ga gidanan sarautar daular a watan Yulin 1816.
Wani mutum mai suna Ali da aka fi sani da Abul Hassan Alasili shi ne ya rubuta kur’anin, wanda ya kammala a ranar 10 ga watan Fabrairu 1564.
Qurnaz ya cea kowace rana yana ware sa’oi 5 zuwa 6 ga wanan aiki na gyaran wannan kwafin kur’ani.
Ya ce tun watanni 6 da suka gabata ya fara aikin, kuma yanzu yana cikin mataki na karshe, kuma da zaran ya kammala, za a mika kur’ani ga bababn dakin ajiye kayan tarihi na kasar Turkiya.