IQNA

Trump Ya Dage Kan Sayarwa Saudiyya Da Makamai

23:54 - July 25, 2019
Lambar Labari: 3483879
Bangaren kasa da asa, shugaban Aurka Donald Trump ya yi watsi da kiran 'yan majalisa na neman dakatarr da sayarwa Saudiyya da makamai.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a

 daren jiya laraba, Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sake hawan kujerar naki kan kudirin da Majalisar dokokin Amurka ta samar na dakatar da sayarwa kasashen Saudiya da hadaddiyar daular larabawa makamai.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, yin watsi da kujerar naki da shugaba Trump ya hau, na bukatar rinjaye da kaso biyu cikin uku na ra'ayin 'yan Majalisar dokokin kasar ta Amurka, wanda kuma hakan nada wuya, ganin yadda wasu 'yan Majalisar na jam'iyar Repablican ke goyon bayan siyasar Trump kan goyon bayan da yake bawa kasar Saudiya.

Kafin hakan dai, Trump ya sanarwa kwamitin tsaro na Majalisar cewa zai sayarwa kasashen Saudiya da Jodan gami da hadaddiyar daular larabawa makamai na dala biliyan takwas bisa abinda ya kira ci gaban barazanar kasar Iran a yammacin Asiya.

 

3829879

 

 

captcha