IQNA

Kwafin Kur'ani Da Aka Fara Bugawa A Makka

23:47 - August 03, 2019
Lambar Labari: 3483907
Bangaren kasa da kasa, an nuna kwafin kur'ani mai tsarki da aka fara bgawa a birnin Makka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya harba cewa, shafin Shabaka Al-arabiyya ya bayar da rahton cewa, cibiyar Sarki Abdulaziz ta nuna wani kwafin kur’ani wanda shi ne farko da aka buga a Makka a 1949.

Wanda ya tsara rubutun kur’anin shi ne Muhammad Taher Kurdi, ya kuma kammala aikin rubutun ne a cikin shekara ta 1949, kuma an buga wannan kwafin kur’ania  cikin wannan shekara.

Cibiyar buga kur’ani ta Makka ta fara aikinta ne ta hanayar samar da kayan aiki da ta saya daga kasar Amurka, haka nan kuma ta samu kwararrun ma’aikata wadanda suka gudanar da wanann aiki na buga kur’ani mai tsarki a wancan lokaci.

Kwafin Kur'ani Da Aka Fara Bugawa A Makka

3831893

 

captcha