IQNA

23:49 - August 03, 2019
Lambar Labari: 3483908
Bangaren kasa da kasa, jakadan Palestine a majalisar dinkin duniya ya nuna wa babban sakataren majalisar Antonio Guterres takaicinsa kan rashin saka Isra'ila cikin masu keta hakkokin yara.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran wafa ya bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar, ya yi dubi kan rahotanni na take hakkokin kananan yara a duniya a cikin shekara ta 2018.

Rahoton na majalisar dinkin duniya ya ce; kananan yara Falastinawa 56 daga cikin 59 da Isra’ila ta kashe a cikin shekara ta 2018 da ta gabata, an harbe su ne kai tsaye da harsasan bindiga masu rai, wanda kuma adadin yah aura na shekara ta 2017.

A cikin shekara ta 2018 Isra’ila ta jikkata kananan yara Falastinawa 1398 a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan, a Gaza kuma ta jikkata 1335, yayin wasu daga cikinsu sun rasa wasu gabban jikinsu.

Rahoton ya ce a halin yanzu kuma akwai kananan yara 203 da suke tsare a cikin gidajen kurkukun Isra’ila ba tare da wani laifi ba.

Rayyad Mansur jakadan Falastinua  majalisar dinkin duniya ya ce, wannan rahoton na majalisar dinkin shi kansa kawai babban dalili ne da ke tabbatar da wajabcin saka Isra’ila a cikin masu take hakkokin kananan yara a duniya.

 

 

3832054

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: