IQNA

23:48 - August 04, 2019
Lambar Labari: 3483912
Bangaren kasa da kasa, hardar kur'ani mai tsarki tun yana karami da samun tarbiyar sufanci na daga cikin siffofin Muhammad Wuld Agazwani.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labaran Alakhbar ya bayar da rahotn cewa, Muhammad Wuld Algzwani, ya hardace kur’ani mai tsarki tun yana dan shekaru biyar da haihuwa.

An haife shia  shekara ta 1965 a garin Bomdid da ke gabashin kasar Mauritaniya, kuma mahaifansa sun kasance daga cikin masu darikar sufaye a kasar, inda ya samu tarbiya a hannunsu.

Algazwani ya karbi takardun shedar kammala karatun digiri na farko, daga nan sai ya shiga aikin soji, inda kuma ya halarci kwasa-kwasai masu yawa a wannan fage.

Kafin zabensa a ranar 22 ga watan Yunin 2019, ya rike mukaman ministan tsaro, da kuma shugaban majalisar tsaron kasa.

Sabon shugaban kasar ta Mauritaniya dai yana bin tafarkin darika ne sau da kafa, kamar yadda dukaknin danginsa suke a kan tafarkin darika.

 

3832219

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: