Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na ioqas.org ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan zama ne bisa kulawar cibiyar kur’ani da sunnah ta duniya, tare da hadin gwiwa da jami’ar Bayero da ke Kano.
Khalid Abdulkafi mataimakin babban sakataren kungiyar kur’ani da sunnah ya bayyana cewa, an gudanar da wannan zama taro tare da halartar malaman jami’a 187 daga jami’oi daban-daban na Najeriya, inda aka gabatar da laccoci 15 a taron.
Ya ce babbar manufar taron ita ce karawa juna sani kan ilmomin kur’ani mai tsarki da kuma yin bahasi kan mu’ujizar kur’ani.
Abdulkafi ya kara da cewa, malamai da masana sun gabatar da kasidu a wurin taron, inda suka fitar da bayanai masu matukar muhimmanci kan wannan bahasi.