IQNA

Azhar Ta Mayar Da Martani Kan Harin Auram

23:55 - August 06, 2019
Lambar Labari: 3483919
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib shugaban cibiyar Azhar ya mayar da martani dangane da hare-haren da aka kai a kusa da cibiyar Auram.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai Almisri yaum, Ahmad Tayyib shugaban cibiyar Azhar ya mayar da martani dangane da hare-haren da aka kai a kusa da cibiyar Auram wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hamsin, tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa koyarwar kur’ani da addini.

Ya ce babu wani dalili da zai halasta wa musulmi kisan jama’a fararen  babu gaira babu sabar a lokacin da suke neman abin da za su ciyar da iyalansu.

Dangane da yadda masu dauke da akidar kafirta musulmi suke danganta abin da suke yi na ta’addanci ga addinin mulsunci, ya bayyana cewa, addinin musulunci baya koyar da ta’addanci, kuma shi ba addinin ta’addanci da tashin hankali da kisan dan adam ba ne.

Malamin ya ci gaba da cewa, a  kowane lokaci musulunci yana kare ran dan adam da bashi kima, ba tare da la’akari da akida ko adininsa ba, domin kuwa jihadi a cikin muslucni yana da matakai, kuma yana zuwa ne a  matsayin kare kai daga masu cutar da musulunci da suke hankoron shafe shi, kuma shi ma yana da ka’ida.

 

3833012

 

 

captcha