IQNA

Ana Ci Gaba Da Mayar Da Martani Kan Shishigin Isra’ila A Lebanon

23:53 - August 25, 2019
1
Lambar Labari: 3483986
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da mayar da martani a kan keta hurumin sararin samaniyar kasar Lebanon da jiragen yakin Isra’ila marassa matuki suka yi a kan Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaban kasar Labanon ya yi tir da harin wuce gona da iri da jiragen yakin Isra'ila suka kai kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar, inda ya ce wannan alama ce ta takalar fada.

Da safiyar yau Lahadi ne kafafen yada labarai suka bayar da rahotannin kakkabo jiragen yakin Isra'ila biyu marassa matuki a yankin kuduncin birnin Beirut bayan wani yunkurin kai hari da suka yi wanda ci nasara ba.

Tashar talabijin din Al-Manar ta ruwaito shugaban kasar Labnon Michel Aoun yayin da yake mayar da martani kan harin na haramtaciyar kasar Isra'ila na cewa; wannan wani sabon makirci ne da nufin yamutsa zaman lafiyar kasar Labnon da ma yankin baki daya.

A nata bangare, Ministar cikin gidan kasar ta Labnon Raya Haffar hasan ta ce wannan hari ya karya hurumin kasar Labnon kuma ya karya doka mai lamba dubu da dari bakawai da daya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shi kuma Ministan harakokin wajen kasar ta Labnon ya ce kasarsa za ta kai karar haramtaciyar kasar Isra'ila gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan yadda take keta hurumin kasar.

Shi ma Shugaban Majalisar koli ta mabiyar mazhanar Shi'a a kasar ta Labnon da Sa'ad Hariri Firayi ministan kasar, dukkaninsu sun yi tir da harin na Isra'ila tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin kasar ta Labnon.

 

3837428

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah wadaida wannan makircin yahudawa
captcha