IQNA

Limamin Tehran: Tattaunawa Da Marassa Cika Alkawali Ba Ta Da Amfani

23:49 - August 30, 2019
Lambar Labari: 3483999
Bangaren siyasa, Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami da ya jagoranc sallar Jumaa a Tehran ya bayyana shiga tattaunawa da wadanda basu cika alkawali da cewa bata da amfani, kamar yadda ya soki kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci da sunan yaki da ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami na’ibin limamin masallacin jumma’a a Tehran, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ce shugaban kasashe masu samarwa da kuma tallafawa kungiyoyin yan ta’adda a duniya, amma abin mamaki ita ce take riya cewa tana yakar yan ta’adda a duniya.

Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami ya kara da cewa shugaban Amurka mai ci a yanzun, ya tabbatar da cewa gwamnatin da ta shude c eta kirkiri kungiyar yan ta’adda ta Daesh a kasashen Iraqi da Syria amma kuma a halin yanzu ita take riya cewa tana yaki day an ta’adda.

A wani bangare na khudubar a yau a Tehran Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa kasar Iran tana daga cikin kasashen da suka fi cutuwa da ayyukan ta’addanci a duniya, musamman a hannun kungiyar munafukai ta Mujahidun Khalk ko MKO, wadanda suka kashe shugaban kasa Dr Ali Rajai da kuma Firaiministansa Hujjatul Islam Muhammad Jawad Bahunar a rana iran ta yau 30 ga watan Augustan shekara ta 1981.

Dangane da hare-haren da Isra’ila ta kai kasar Lebanon kuma Aya. Khatami ya ce ya dace a maiyar mata da martini don kada hakan ya ci gaba.

Sai kuma dangane da musulman yankin Kashmir na kasar India, Hojjatol Islam Sayyid Ahmad Khatami ya ce yakamata gwamnatin kasar India ta yi masu adalci.

3838599

 

 

 

captcha