IQNA

Haniyya: Muna Tare Da Kasar Iran A Gwagwarmayar Da Take Yi Da Masu Girman Kai Na Duniya

23:51 - September 01, 2019
Lambar Labari: 3484006
Bangaren siyasa, shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya aike da wata wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Isma’il Haniya shugaban Offishin Siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas dake yankin palasddinuya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aikewa jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i inda ya godewa Jagoran game da tarbar da aka yi wa tawagar kungiyar ta Hamas da ta kai masaziyara,kana ya jinjina game da cikakken goyon bayan da jagoran yake bawa yan gwagwarmayar Palasdinu,

Har ila yau Haniya ya kara da cewa babu gudu babu ja da baya suna tre da Iran a ci gaba da gwagwarmayar da suke yi ta kwatar yancinsu har sai hakar su ta cimma ruwa,

Haka nan ya kara da cewa bayanan da jagoran yayiwa tawagar hamas dinta kara musu karfin guiwa da kara dakewa , kuma sun tasirantu sosai wajenci gaba da jajircewa a gwagwarmayar da suke yi da babban makiyi haramtacciyar kasar Isra’ila.

A kwanakin baya ne wata babbar tawaga da ta kunshi manyan kusoshin kungiyar Hamas ta gudanar da wata ziyara ta tsawon kwanakia  kasar Iran, inda ta gana da jagoran juyin juya hali da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.

A yayin wannan ziyara tawagar ta Hamas ta kara jaddada matsayinta na tsayawa a sahu guda tare da Iran wajen fuskantar masu girman kai da ke nufin rusa al’ummar muuslmi da yankin gabas ta tsakiya.

3839165

 

captcha