Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren majalisar Karbala Hussain Alabbudi ya bayyana cewa, an hana shawagin jirage marassa matuki a Karbala a ranar ashura saboda dalilai na tsaro.
Ya ce an dauki wannan matakin ne saboda dalilai na tsaro ga tarukan ashura wanda miliyoyin musulmi suke taruwa a birnin mai alfarma.
Ya kara da cewa, an dauki kwaran matakan tsaro a ciki da wajen birnin domin bayar da kariya ga masu tarukan ziyara a ranar Ashura a birnin na Karbala a wannan rana.
Dangane da matakin hana shawagin jirage marassa matuki kuwa, ya ce wannan hada da jiragen yaki da ma wadanda ban a yaki ba, kuma babu wani jirgi mai matuki ko maras matuki da za a bari ya nufi inda haramin Imam Hussain (AS) da na Abbas (AS) suke.
Ya kammala da cewa a halin yanzu an kammala dukkanin abubuwan da suka kamata na matakan tsaroa dukkanin fadin birnin.