IQNA

UN: Manufar Gwamnatin Myanmar Ita Ce Kisan Kiyashi Kan Rohingya

23:05 - September 17, 2019
Lambar Labari: 3484060
Bangaren kasa da kasa, rahoton majalisar dinkin duniya ya tabbatar da cewa gwamnatin Myanmar ta yi kisan kiyashi kan musulmin Rohingya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce musulmai yan asalin Rohingya da suka rage a kasar Myanmar na fuskantar hadarin kisan kare dangi, tare da bayyana cewa a halin da ake ciki mayar da duban yan Rohingyar dake gudun hijra a kasashen ketare gida na tattare da hadarin gaske.

Kwamitin bincike da hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a shekarar da ta gabata, ya bayyana ayyukan da sojin suka yi a shekarar 2017 a matsayin kisan kare dangi.

Akalla yan Rohingya dubu 740 ne suka tsere daga kauyukan su sakamakon kona gidajen su da aka yi, wadda a ta dalilin haka ne aka kashe da dama daga cikin su, aka yi wa wasu fyade, wasu kuma suka fuskanci cin zarafi a sansanonin yan gudun hijirar Bangladesh inda suka nema mafaka.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce al’ummar Rohingya dubu 600, wadanda a halin yanzu ke makale a cikin jihar Rakhine na Myanmar na cikin mayuwacin hali.

A binciken su na karshe kan barazanar da al’ummar Rohinya ke fuskanta da aka gabatar a birnin Geneva, Majalisar Dinkin Duniya ta ce gwamnatin Myanmar ta cigaba da kauda kai ga irin hallayar wariya da nuna gyama da al’ummar musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke fuskanta wanda hakan na iya jawo ci gaba da kisan gare-danga nan gaba.

3842644

 

 

 

captcha