IQNA

Sulhu Tsakanin Addinai A Gidan Radiyon Najeriya

22:59 - September 21, 2019
Lambar Labari: 3484071
An Gabatar da wani shiri ma taken sulhu tsakanin addinai a gidan radiyon Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, Sayyid Mahmud Azimi Nasabadi shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Najeriya ya halarci wani shiri a gidan radiyon Najriya mai taken sulhu tsakanin addinai.

A lokacin da yake gabatar da bayaninsa a cikin shirin, karamin jakadan na Iran a Njeriya ya bayyana zaman lafiya da juna tsakanin musulmi da kirista a matsayin wajibi, domin kuwa dukkaninsu addinai da aka saukar daga sama.

Ya ce addinin muslunci ya koyar da musulmi zaman lafiya tare da dukkanin sauran mabiya addinai tare da fahimtar juna, wanda kuma hakan shi ne koyarwar dukkanin annabawa, girmama dan adam da kuma nuna masa kyawawan dabiu.

Sayyid Mahmud Azimi ya bayyana cewa, rayuwar manzon Allah cike take da darussa ga dukkanin muuslmi, yadda ya zauna da mutane mabiya addinai daban-daban ba tare da ya cutar da sub a, kuma wasu da dama sun karbi addininsa saboda kyawawan dabiu da suka gani daga gare shi, wanda kuma hakan ita ce koyawar dukkanin annabawa.

 

 

3843545

 

 

 

captcha