Kamfanin dillancin labaran iqna tashar talabijin ta Almasirah daga kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau jiragen yakin masarautar Saudiyya sun yi ruwan bama-bamai a yankin Sauda, inda suka ragargaza wani masallaci a kauyen, inda suka kashe fararen hula 5 dukkaninsu iyalan gidan guda.
Rahoton ya ce mutanen sun fito daga cikin gidansu ne suka fake a cikin domin kaucewa hare-haren jiragen yakin na Saudiya, amma kuma jiragen suka harba makamai a kan masallacin, wanda hakan ya ragargaza ginin masallacin tare da kashe mutane da ke ciki, da suka hada har da kananan yara guda biyu.
Wannan na daga cikin irin hare-haren da Saudiyya ta kwashe tsawon kimanin shekaru biyar tana kaddamarwa a kan al’ummar kasar Yemen, inda ta kashe dubban fararen hula kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tabbatar.
A halin yanzu mayakan sa kai na kasar Yemen sun fara mayar da martani kan irin wadannan hare-hare, martanin baya-bayan nan shi ne wanda suka kaddamar kan kamfanin mai na Aramco na kasar Saudiyya, wanda ya yi sanadiyayr mayar da man da kasar take fitarwa zuwa kasa da rabi a halin yanzu.