IQNA

Majami'o'in Australia Sun Ki Amincewa Da Gina Makarantar Musulunci

16:04 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1781983
Bangaren kasa da kasa: Jagororin mabiya addinin kirista na mazhabar Angalican sun ki amincewa da batun gina makarantar addinin musulunci a birnin Sydney fadar mulkin kasar Australia, wanda wannan shi ne karo na farko da suka taba nuna irin wannan hali ga al'ummar musulmi da ke zaune a kasar ta Australia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Iba cewa; Jagororin mabiya addinin kirista na mazhabar Angalican sun ki amincewa da batun gina makarantar addinin musulunci a birnin Sydney fadar mulkin kasar Australia, wanda wannan shi ne karo na farko da suka taba nuna irin wannan hali ga al'ummar musulmi da ke zaune a kasar ta Australia. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar kotun kolin kasar ta Austaralia ta baiwa musulmi damar gina wannan makaranta amma kuma a lokaci guda jagororin mabiya addinin kirista suka saka kafa suka yi fatali da dukkanin takardun da kotun ta bayar domin bayar da izinin gina wannan makaranta. Wannan dai wani mataki na hana ci gaban da musulmi suke samu a cikin al'ummar kasar Australia.

409094
captcha