IQNA

An Bude Baje Kolin Kayayyakin Taswiar Musulunci A Malazia

16:57 - September 12, 2009
Lambar Labari: 1825199
Bangaren kasa da kasa; An bude wani baje kolin kayayyakin taswirar Musulunci a karkashin wani shiri na hadin gwiwa tsakani Turkiya da Malazia, a jami'ar kimiyya ta kasar Malazia.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na jami'ar MARA cewa; An bude wani baje kolin kayayyakin taswirar Musulunci a karkashin wani shiri na hadin gwiwa tsakani Turkiya da Malazia, a jami'ar kimiyya ta kasar Malazia, Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli yana samun halartar daliban jami'a daga sassa daban-daban na kasar, musamman ma masu gudanar da bincike daga cikinsu kan harkokin addinin Musulunci. Daga cikin muhimman abubuwan da aka baje kolinsu akwai hotun da ke nuna muhimman abubuwan da suka wakana a cikin tarihin addinin Musulunci, da kuma taswirar kasashen musulmi da suka hada da na gabacn na hiyar Asia da kuma yankin gabas ta tsaki gami da Afirka.
463498






captcha