IQNA

An Bude Wasu Ajujuwan Koyar Da Addini A Kasar Zambia

10:32 - September 05, 2010
Lambar Labari: 1987532
Bangaren kur'ani; An bude wasu ajujuwan koyar da wasu daga cikin hukunce-hukuncen addinin Musulunci a kasar Zambia, da nufin ilmantar da musulmin kasar kan muhimmancin azumi a addinace da kuma a ilmance.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar bunkasa harkokin al'adu da iolmomin Musulunci ta Iran cewa, an bude wasu ajujuwan koyar da wasu daga cikin hukunce-hukuncen addinin Musulunci a kasar Zambia, da nufin ilmantar da musulmin kasar kan muhimmancin azumi bisa abin da ilmi ya tabbatar da shi.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bangaren kula da harkokin ilimi na reshen wannan cibiya ne da ke kasar ta Zambia ya dauki nauyin shirya bayar da wannan horo na musamamn ga wasu daga cikin musulmin kasar.

Zambia dai daya ce daga cikin kasashen da ke kudancin nahiyar Afirka, da take samun ci gaba matuka wajen karbar addinin Musulunci, duk kuwa da cewa akasarin mutanen kasar kirista ne.

647262
captcha