IQNA

An Gudanar Da Taron Girmama Mahardata Kur'ani A Masar

10:44 - September 07, 2010
Lambar Labari: 1989318
Bangaren kasa da kasa; An gudanar da zaman taro na shekara-shekara a kasar Masar da ake girmamam mahardata kur'ani mai tsarki na kasar, inda aka girmama mahardata 400 a garin saf da ke kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ta nakalto daga jaridar kasar ta yaum sabiu an habarta cewa, an gudanar da zaman taro na shekara-shekara a kasar Masar da ake girmamam mahardata kur'ani mai tsarki na kasar, inda aka girmama mahardata 400 a garin saf.

Wannan zaman taron dai kwamitin kula da ayyukan kur'ani na birnin Saf ne ya dauki nauyin shirya shi tare da halartar wakilan kungiyoyin addini da cibiyoyi, da suka hada da jami'ar Azhar da kuma ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar masar.

An gabatar da jawabai ga mahalarta taron kan muhimmancin bunkasa ayyuka na kur'ani musamman ma a tsakanin matasan kasar.

649815

captcha