IQNA

An Yi Kira Zuwa Ga Hadin Kai Tsakanin Musulmi A gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa

16:03 - January 11, 2011
Lambar Labari: 2063011
Bangaren kasa da kasa, Babban jami’i mai kula da bangaren harkokin ilimi da yada al’adun muslunci a kungiyar ISESCO ya bayyana matukar gamsuwarsa dangane da gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin mashhad na kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yada labaransa daga lardin Khorasan an bayyana cewa, babban jami’i mai kula da bangaren harkokin ilimi da yada al’adun muslunci a kungiyar ISESCO ya bayyana matukar gamsuwarsa dangane da gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin mashhad baban birnin lardin Khorasan.
Abbas Sadri wanda shi ne babban jami’i kuma wakilin kungiyar ISESCO a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, gasar tana matukar muhimmanci, kuma yadda aka shiryata babban abin burgewa ne, domin kuwa tana samun halartar wakilai daga kasashen duniya arba’in.
Babban jami’i mai kula da bangaren harkokin ilimi da yada al’adun muslunci a kungiyar ISESCO ya bayyana matukar gamsuwarsa dangane da gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin mashhad.
727867

captcha