IQNA

Malamin Kirista Mai Wulakanta Kur'ani Zai Yi Taro Kan Hukunci A kan Kur'ani

10:23 - January 13, 2011
Lambar Labari: 2063853
Bangaren kasa da kasa, Malamin kiristan nan na kasar Amurka day a shahara wajen wulakanta kur'ani mai tsarki, zai gudanar da wani taro da ya kira ranar duniya ta hukunci dangane da kur'ani, a wani sabon salon wulakanta littafi Allah mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na My fox Orlando an habarta cewa, mMalamin kiristan nan na kasar Amurka day a shahara wajen wulakanta kur'ani mai tsarki, zai gudanar da wani taro da ya kira ranar duniya ta hukunci dangane da kur'ani, a wani sabon salon wulakanta littafi Allah mai tsarki a idon duniya.

Mutumin mai suna Terry Jonse a cikin shekarar da ta gabata ne ya ayyana ranar 11 ga watan kowane satumba a matsayin ranar kone kur'ani mai tsarki ta duniya, lamarin day a fuskanci kakakusar suka daga musulmi da ma mabiya addinin kirista daga sassa daban-daban na duniya.

Malamin kiristan na kasar Amurka da ya shahara wajen wulakanta kur'ani mai tsarki, zai gudanar da wannan taron ne da ya kira ranar duniya ta hukunci dangane da kur'ani, a wani sabon salon wulakanta littafi Allah mai tsarki, da nufin kara samun suna a kafofin yada labarai.

729169



captcha