IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Mai Tsarki Ta Kasar Oman

14:29 - February 01, 2011
Lambar Labari: 2074098
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar kula da ayyukan shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Oman ta sanar da shirin fara gudanar da gasa ta kasa a karo na ashirin da daya, wadda ake sa ran gudanarwa a cikin watanni uku masu kamawa a nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na oman tribune an habarta cewa, cibiyar kula da ayyukan shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Oman ta sanar da shirin fara gudanar da gasa ta kasa a karo na ashirin da daya, wadda ake sa ran gudanarwa a cikin watanni uku masu kamawa a nan gaba, tare da halartar malamai da kuma jami’an kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wanann gasa tana daga cikin irinta masu muhimmanci da ake gudanarwa a cikin kasashen larabawa da syuka hada da larabawan yankin gabas ta tsakiya a kowace shekara. Kasar Oman na daga cikin kasashen larabawan yankin da suke daukar nauyin shiray gasar karatu da hardar kur’ani ta kasa da kasa.
Cibiyar kula da ayyukan shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasar Oman ta sanar da shirin fara gudanar da gasa ta kasa a karo na ashirin da daya, wadda ake sa ran gudanarwa a cikin watanni uku masu kamawa a nan gaba, da zai kama cikin watan Afirilu.
739557

captcha