IQNA

Musulmin Tailand Sun Gudanar Da Taron Goyan Bayan Al'ummar Masar

15:56 - February 06, 2011
Lambar Labari: 2076301
Bangaren siyasa da zamantakewa: bangarori daban-daban na musulmin kasar tailand a ranar sha biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun gudanar da wani taron gangami na nunawa al'ummar Masar cewa suna tare da su a wannan kokari da gwagwarmaya da suka nuna na fuskantar zalunci da danniyar Mubarak kuma sun gudanar da wannan taron gangami a gaban ofishin jakadancin Masar a babban birnin Tailand Bankuk.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; bangarori daban-daban na musulmin kasar tailand a ranar sha biyar ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun gudanar da wani taron gangami na nunawa al'ummar Masar cewa suna tare da su a wannan kokari da gwagwarmaya da suka nuna na fuskantar zalunci da danniyar Mubarak kuma sun gudanar da wannan taron gangami a gaban ofishin jakadancin Masar a babban birnin Tailand Bankuk. Al'ummomi da dama kuma daban daban a kasashen duniya ke gudanar da irin wannan zanga-zanga ta nuna goyan bayan al'ummar kasar masar da ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna Allah wadai dab akin mulkin danniya na Husni Mubarak wanda ya share shekaru talatin a kan karagar mulkin kasar ta Masar cikin zalunci.

741481

captcha