IQNA

Taron Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinan Musulunci Da Kuma Kirista A Beirut

15:04 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109231
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da zaman taron tattaunawa tsakanin mabiya addinan kirista da na muslunci a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, tare da halartar wakilan dukkanin bangarorin biyu, da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya wadannan addinai biyu masu tarihi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles cewa, ana shirin fara gudanar da zaman taron tattaunawa tsakanin mabiya addinan kirista da na muslunci a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, tare da halartar wakilan dukkanin bangarorin biyu, da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya wadannan addinai biyu masu tarihi a duniya.
Rahoton ya kara da cewa a wani bangare kuma an gudanar da wani zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, dangane da hanyoyin habbaka ttatalin arzikin kasashen muslumi da kuma yadda zai yi tasiri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya, ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba, ta yadda zai taimaka wajen warware da dama daga cikin irin wadannan matsaloli.
Yanzy haka dai ana shirin fara gudanar da zaman taron tattaunawa tsakanin mabiya addinan kirista da na muslunci a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, tare da halartar wakilan dukkanin bangarorin biyu, da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya wadannan addinai biyu.
777118

captcha