IQNA

Dukkanin Ayyukan Imam Khomeini Ya Ginu Ne A kan Koyarwar Kur'ani

11:11 - June 04, 2011
Lambar Labari: 2133069
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin masu halartar taron tunawa da zagayowar cika shekaru 22 da wafatin marigayi Imam Khomeini (RA) jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya bayyana cewa dukkanin ayyukan Imam sun ginu ne a kan koyarwar kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, Muhammad Taqi daya daga cikin masu halartar taron tunawa da zagayowar cika shekaru 22 da wafatin marigayi Imam Khomeini (RA) jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya bayyana cewa dukkanin ayyukan Imam sun ginu ne a kan koyarwar kur'ani mai tsarki, wanda kuma shi ne babban sirrin samun nasararsa.

Malamin wanda daya ne daga cikin fitattaun malaman addinin Musulunci kuma masana a kasar Bama, ya bayyana cewa Imam Khomeini (RA) ya bayar da gudunmawa ga al'ummar muslumi, wadda har duniya ta nade ba za a taba mantawa da shi ba, domin kuwa ya kafa tafarki na yin aiki da koyarwar addinin muslunci tare da fadakar da al'ummar musulmi nauyin da ya rataya kansu.

Daya daga cikin masu halartar taron tunawa da zagayowar cika shekaru 22 da wafatin marigayi Imam Khomeini (RA) jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya bayyana cewa dukkanin ayyukan Imam sun ginu ne a kan koyarwar kur'ani mai tsarki.

803233
captcha