IQNA

Tarukan Tunawa Da Ranar Hijabi Ta Duniya A kasar Pakistan

18:24 - September 06, 2011
Lambar Labari: 2182595
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wasu taruka na musamman na tunawa da ranar hijabi ta duniya wanda wata babbar cibiyar bunkasa harkokin muslunci da al'adu a kasar Pakistan ta dauki nauyin shiryawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya samu rahoto shafin yanar gizo na The News cewa, wasu taruka sun gudana na musamman na tunawa da ranar hijabi ta duniya wanda wata babbar cibiyar bunkasa harkokin muslunci da al'adu a kasar Pakistan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa da nufin kara wayar da kan musulmi kan muhimamnci saka tufafin muslunci.

Wannan aya mai albarka tana yin nuni ne da cewa ma'abota hankali su ne wadanda suke tuna Allah da ambatonsa tare da yin tunani a cikin halittar sammai da kassai, domin kuwa sun san wannan duniya da abin da ke cikinta ba wai kawai tana da mahalicci ba ne, a'a shi mahaliccin ya yi ta ne da wata manufa.

Ya kuma yana tafiyar da ita kan tsari na musamman, kamar yadda mutum kan gina gida, yana yin hakan ne da manufa ta musamman, da kuma tsarin da yake son gidan ya kasance, idan mutum ya fahimci cewa lallai Allah madaukakin sarki mahaliccin kowa da komai ya halicci duniya ne da wata manufa ta musamman.

To a nan kuma mutum zai riski cewa to mu kanmu da muke a cikin duniyar Allah bai halicci mu kawai domin cike wuri ba, kuma bai bar rayuwarmu kara zube ba, yana da manufar halittarmu, da kuma tsari day a dora rayuwarmu a kai na dabi'a, da kuma tsari na dokoki da yake son rayuwarmu ta tafi a kansa.

854747


captcha