IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Mayar Da Martani Kan Pira Ministan Canada

17:02 - September 15, 2011
Lambar Labari: 2187783
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta mayar da martini kan pira ministan kasar Canada dangane da fusrucin tozarta addinin muslunci da a fito daga bakinsa, tare da yin Allawadai da shi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto rahoto daga shafin sadrawa na OCI cewa, kungiyar ta mayar da martini kan pira ministan kasar Canada StephenHarper dangane da fusrucin tozarta addinin muslunci da a fito daga bakinsa, tare da yin Allawadai da shi da kuma kiransa da ya shiga taitayinsa.
A bangare guda kuma Kungiyar kasa da kasa mai kare hakkokin kananan yara da fada-fadan coci suka yi lalata da su ta bukaci kotun kasa da kasa mai hukumta manyan laifufffuka da ta gurfanar da Paparoma Benedict na 16 a gabanta da zargin laifin cin zarafin bil'adama.
Ita dai wannan kungiya wacce take birnin hicago na kasar Amurka ta ce ta shigar da kara zuwa ga kotun kasa da kasar inda ta bukaci kotun da gurfanar da Paparoman da wasu manyan jami'an fadar Vatican su uku saboda hannun da suke da shi cikin laiffuffukan cin zarafin bil'adama da suka hada da fyade da sauran ayyuka na lalata a duk fadin duniya baki daya.
A cikin wata sanarwa da lauyoyin kungiyar suka fitar sun bayyana cewar manyan jami'an fadar Vatican din suna sane da cin zarafi da lalata da dubun dubatan mutane mafiya yawansu kananan yara da malaman coci suke yi amma kuma sun rufe lamarin. Har ila yau lauyoyi sun aike wa kotun wasu bayanai cikin sama da shafuka da suke nuni da irin danyen aikin da malaman kiristan suka yi tsawon shekarun da suka gabata.
860720

captcha