Bangaren kasa da kasa; Sheikhul Azzahar ya yi nuni da matsayi da daukakar addinin musulunci a tsakanin jama'a a yau da jaddada cewa: juyin da sauyin da aka samu a kasar Masar bayan ya sake maido da matsayi da rawar da addinin musulunci ke takawa a tsakanin jama'a a wannan kasa ya kuma sake falfado da kare martabar addini a cikin zukatan al'ummar wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Sheikhul Azzahar ya yi nuni da matsayi da daukakar addinin musulunci a tsakanin jama'a a yau da jaddada cewa: juyin da sauyin da aka samu a kasar Masar bayan ya sake maido da matsayi da rawar da addinin musulunci ke takawa a tsakanin jama'a a wannan kasa ya kuma sake falfado da kare martabar addini a cikin zukatan al'ummar wannan kasa.Ahmad Altaib sheikhul azzahar a kasar Masar a ranar ashirin da hudu ga watan Meher na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan kammala wani taron masana da manazarta na kasar Masar ya jaddada cewa; addinin wani gimshiki ne na asali a al'adun al'ummar kasar Masar dab a za a iya raba al'ummar kasar ta Masar da shi ba.
881377