IQNA

An Gudanar Da Taron Idul Gadir A Birnin Vienna Na Kasar Austria

21:30 - November 17, 2011
Lambar Labari: 2223872
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musumi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma wasu daga cikin masu bin tafarkin sunna ne suka halarci taron idil Gadir da aka gudanar a birnin Vienna.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daruruwan musumi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma wasu daga cikin masu bin tafarkin sunna ne suka halarci taron idil Gadir da aka gudanar a birnin Vienna babban birnin kuma fadar mulkin kasar Austria.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron ne tare da halartar musulmi da dama, inda aka gabatar da laccoci dangane da matsayin wannan rana mai albarka, da kuma abubuwan da suka faru a cikinta, musamman ma bayyana Imam Amirul muminin a matsayin khalifan manzon Allah, wanda manzo ya yi da kansa a Gadir Khum.
Bayanin ya tabbatar da cewa, daruruwan musumi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da ma wasu daga cikin masu bin tafarkin sunna ne suka halarci taron idil Gadir da aka gudanar a birnin, bayan sauraron laccoci an ci abinci aka waste.
899176


captcha