IQNA

Karfin Kungiyar Hamas Ya Kawo Karshe

14:06 - January 01, 2012
Lambar Labari: 2249126
Bangaren kasa da kasa: a daidai lokacin da karfi da matsayin kungiyoyin gwagwarmaya nna labanon da na palasdinu ke kara samin gurin zama da karbuwa da karfafa masu guiwa a wannan lokaci na fadakar musulmin yankin sai gashi ministan harkokin wajen kasar Katar kuma firaministan kasar a wani bayani na ban dariya da mamaki kuma da babu wanda zai karba ya bayyana cewa; karfin da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a Palasdinu ya kawo karshe.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a daidai lokacin da karfi da matsayin kungiyoyin gwagwarmaya nna labanon da na palasdinu ke kara samin gurin zama da karbuwa da karfafa masu guiwa a wannan lokaci na fadakar musulmin yankin sai gashi ministan harkokin wajen kasar Katar kuma firaministan kasar a wani bayani na ban dariya da mamaki kuma da babu wanda zai karba ya bayyana cewa; karfin da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a Palasdinu ya kawo karshe.Hamid bin Jasim ministan harkokin wajan kasar katar da kasarsa ke bin manufar siyasar Amerika da haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin a birnin Alkahira a daidai wani guri na taruwar masu adawa da gwamnatin Suriya ya raya cewa; kungiyar gwagwarmaya ta palasdinu Hamas karfinta ya kawo karshe a matsayinta na kungiya mai dauke da makami har ila yau fitar Hamas daga birnin Damaskos ya zama tabbas da kuma ke nufin kawo karshen kungiyar Hamas da kuma ta Ikhwanul Musulim a Jodan da Masar saboda da matsalolin cikin gida a kasashensu.


926220

captcha