IQNA

Imam Musa Sadr Ya Kasance A Raye Har Zuwa Shekara Ta 1994

21:52 - January 29, 2012
Lambar Labari: 2264416
Bangaren kas ada kasa, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Imam musa Sadr ya kasance a raye a cikin gidan kurkun Gaddafi har zuwa shekara ta 1994, kuma batun shigarsa cikin kasar Italia tare da abokan tafiyarsa babu gaskiya a cikins.

Kamfanin diallcnin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, bayanai sun tabbatar da cewa Imam musa Sadr ya kasance a raye a cikin gidan kurkun Gaddafi har zuwa shekara ta 1994, kuma batun shigarsa cikin kasar Italia tare da abokan tafiyarsa babu gaskiya a cikin hakan, kamar dai yadda wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar Libya suka tabbatar.
Wannan bayani kuwa an same shi ne bayan da wata tawaga daga kasar Lebanon ta nufi kasar Libya, kuma take ci gaba da bin kadun makomar Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa biyu da suke tare das hi a wancan lokacin, bayanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi ya aike masa da goron gayyata, kuma daga nan ba a sake jin duriyarsa ba.
Imam Musa Sadr ya taka gagarumar rawa wajen hada kan al'ummar kasar Lebanon, musamman ma tsakanin shi'a da sunna, da kuma musulmi da kiristoci, lmarin day a yi bababn tasiri a tsakanin al'ummar wannan kasa.
941552


captcha