IQNA

Samun Fahimtar Juna Tsakanin Hizbullah Da Amal Kokari Ne Ayatollah Khamnei

18:07 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275349
Bangaren kasa da kasa, samun fahimtar juna tsakanin kungiyoyin Hizbullah da kuma Amal a kasar Lebanon da ake gani a halin tsakanin jagororin kungiyar sakamako ne na jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamnei.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wata zantawa da ta hada shi da mamba a kungiyar Amal Khalil Hamadan ya bayyana cewa, samun fahimtar juna tsakanin kungiyoyin Hizbullah da kuma Amal a kasar Lebanon da ake gani a halin tsakanin jagororin kungiyar sakamako ne na jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamnei Allah ya kare shi tare da kara masa tsawon kwana.
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahil-uzma Sayyid Ali khamnei wanda ya gabatar da wajabi ga jami'an gwamnatin kasa a ranar 30 ga watan yuni ya tabo batun yunkurin al'ummar kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afirka. Ya bayyana yunkurin a matsayin farkawar musulmi da komawa zuwa ga musulunci wanda shi ne hanyar sa'adar al'ummar musulmi. Dangane da yunkurin al'ummar Masar da Tunisiya, jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana su a matsayin wani gagarumin sauyi acikin tsarin siyasar zalunci da cin zarafin bil'adama. Kuma yana a matsayin bude wani sabon shafi ne a cikin wannan yankin.
Jagoran Juyin musuluncin da ya ke yin bayanin halayyar girman kai na kasashen yammacin turai ya ce: "A wannan lokacin kasashen yammacin turai masu girman kai, suna cikin matsanancin hali domin kuwa ba su son su fuskanci hakikanin abinda ya ke faruwa na cewa al'umma sun farka. Ba su kuma son su gaskata cewa al'umma sun koma suna riko da musulunci. Sai dai wannan shi ne hakikanin abinda ya ke faruwa a kasa" Ruhin musulunci ne ya sake dawowa acikin kasashen musulmi. Gwamnatocin wadannan kasashen da su ke damfare da Amurka da kuma yammacin turai sun ci zarafin al'ummunsu ta yadda su ka ingiza al'ummar zuwa ga yin bore. Ba su barwa al'umma wani zabi ba da ya wuce yin juyi wanda shi ne kadai hanyar kalubalantarsu. Shi ne abinda ya sa su ka yunkura kuma suna ci gaba da yunkuri. Shakka babu kuma wannan yunkurin zai kai ga samun nasara.
953640

captcha