Bangaren siyasa da zamantakewa: Husein Diyusalar a wata ziyara day a kai kuduncin kasar Pilifine domin halartar wani taro da tarurruka iri iri kan bayyanawa da fayyace irin nauyi da matsayin mata da suka rataya a wuyansu a daidai wannan lokaci na fadakar da al'ummar musulmi da duk dan adam baki daya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Husein Diyusalar a wata ziyara day a kai kuduncin kasar Pilifine domin halartar wani taro da tarurruka iri iri kan bayyanawa da fayyace irin nauyi da matsayin mata da suka rataya a wuyansu a daidai wannan lokaci na fadakar da al'ummar musulmi da duk dan adam baki daya. Husein Diyosalar a wannan ziyara ta shi yayi ganawa da dama da mahukumta da manyan mutane da shugabannin al'umma da na siyasa da bangaren al'adu kamar wasu shugabannin cibiyoyin al'adu da kuma halartar tarurrukan da suka shafi tunawa da ranekun haifuwar Fatimatul Zahra (AS) da imama Khomeini Mu'assasin juyin juya halin musulunci a jamhuriyar musulunci ta Iran kuma ya ziyaci Darul Kur'an a masallacin Imam Ali (AS) a garin Marawi inda ya kaddamar da bude wannan masallaci. A ranar asabar ashirin da uku ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya ne a hubbarin jami'ar Mindanu'u babbar jami'a ta gwamnatin kasar Filipine aka gudanar da taro kan mace da kuma dangantakarta da fadakarwa da =ci gaban al'umma.
1011208