IQNA

Jami’ar Azahar Ta Yi Allawadai Da Sabon Salon Kiyayya Da Musulunci

22:46 - September 12, 2012
Lambar Labari: 2410345
Bangaren kasa da kasa, jami’ar Azhar ta Masar ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da sabon salon da aka bullo da shia acikin kasashen yammacin turai na nuna tsananin kiyayya da addinin musulunci da kuma yin amfani da hakan a matsayin wani makami na siyasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Diyar cewa, jami’ar Azhar ta Masar ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da sabon salon da aka bullo da shia acikin kasashen yammacin turai na nuna tsananin kiyayya da addinin musulunci da kuma yin amfani da hakan a matsayin wani makami na siyasa kamar yadda ake gani a halin yanzu.
wasu daga cikin malaman sunna sun yi kakkausar suka kan malamin wahabiyawan Saudiyya wanda ya ci zarafin manzon Allah da addinin musulunci ta hanyar bayyana abin da ya ga dama a cikin son ransa da sunan yana bayyana matsayar addini ko kuma fatawa.
A wani labarin na daban kuma an sheda cewa kasar Siriya ta shaida cewar ba za ta janye dakarunta ba daga cikin garururwan da yan tawaye masu dauke da makamai suke, sai ta samu tabbaci daga yan bindigar a rubuce na cewar sun daina kai hare-hare, a cewar ministan harakokin wajen kasar ta Siriya a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta nuna cewa, fadar cewar kasar Siriya za ta janye daga cikin garururwan da suka mamaye kafin ranar 10 ga wannan wata ba gaskiya bane, manzon majalisar dinkin duniya da kungiyar larabawa Kofi Anan, har yanzu bai bamu tabbaci ba a rubuce na cewar sun amince da shirin na sa za su daina kai hare-haren ta'adanci daga bangaren yan adawar ba, da kuma aniyarsu ta maika makaman nasu.
Kuma Kofi Anan, bai bamu tabbaci a rubuce ba na cewar kasashen Qatar, Saudiya, da Turkiya, za su daina bada kudin ga kungiyoyin ta'adancin ba, wadannan kasashe sun sun taimakama yan adawar kasar ta Siriya sosai inda har kasashen Qatar da saudiya ke kira a ba yan adawar makama.

1096681
captcha