IQNA

Taron Tunawa Da Shahadr Imam Sadiq (AS) A Birnin Vienna Na Kasar Austria

22:48 - September 12, 2012
Lambar Labari: 2410352
Bangaren kasa da kasa, an sanar cewa za a gudanar da zaman taro na tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Sadiq (AD) a birnin Vienna na kasar Austria wanda babbar cibiyar muslunci ta birnin ta dauki nauyin shirya da gudanarwa tare da halartar masana .
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an sanar cewa za a gudanar da zaman taro na tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Sadiq (AD) a birnin Vienna na kasar Austria wanda babbar cibiyar muslunci ta birnin ta dauki nauyin shirya da gudanarwa tare da halartar masana daga sassa na kasar.
Wani malami ya bayana cewa a mahangar Imam Ja’afar Sadiq (AS) tassubanci shi ne babban musabbabin rarrabar kai tsakanin mabiya addinin muslunci wanda da ace musulmi za su gane cewa abin da ya hada su ya fi wanda ya raba su to da an warware matsaloli da dama da suka hada rashin hadin kai da kuma rarraba a tsakaninsu.
Daya daga cikin malaman jami’oin Pakistan ya bayyana cewa Imam Jafar Sadiq ba daya ne kawai daga cikin limaman ahlul baiti ba shi ya kasance malami na dukkanin musulmi sunna da shi’a domin shi ne wanda ya raya ilimi da dukkanin al’ummar musulmi suke amfana da shi a dukkanin mazhabobi ko da kuwa an samu banbanci da yadda shi ya koyar amma dai shi ne tushe.

1096204

captcha