IQNA

Mahukuntan Libya Sun Yi Tayin Makudan Kudi Domin Rufe Batun Imam Musa Sadr

23:38 - September 24, 2012
Lambar Labari: 2419000
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Libya sun bukaci bayar da wasu kudade da suka kai dala biliyan guda ga gwamnatin kasar Lebanon domin rufe batun bincike kan makomar Imam Musa Sadr wanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar na yi sanadiyar bacewarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mahukuntan kasar Libya sun bukaci bayar da wasu kudade da suka kai dala biliyan guda ga gwamnatin kasar Lebanon domin rufe batun bincike kan makomar Imam Musa Sadr wanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar na yi sanadiyar bacewarsa tare da abokan tafiyarsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka a yankin.
1105205



captcha