IQNA

Wasu Malaman Jami'ar Azhar Sun Bukaci A Kwace Takardun shedar Zama dan masar Daga Qardawi

15:11 - July 31, 2013
Lambar Labari: 2569408
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman addinin muslunci a jami'ar Azhar ta kasar Masar sun bukaci da a kwace takardun shedar zama dan kasa daga hannun Yusuf Qardawi malamin gwamnatin Qatar wanda ya taka gagarumar rawa wajen haifar da fitina akasar ta Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, da dama daga cikin malaman addinin muslunci a jami'ar Azhar ta kasar Masar sun bukaci da a kwace takardun shedar zama dan kasa daga hannun Yusuf Qardawi malamin gwamnatin Qatar wanda ya taka gagarumar rawa wajen haifar da fitina a kasar ta Masar da ma wasu daga cikin kasashen larabawa.

A bangare guda kuma Shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adli Mansur ya bayyana cewa ba ya da niyyar kafa dokar ta baci a kasar, kuma yana kokarin ganin kasar ta koma kan sahihin tafarki na demokradiyya da zai hada dukkanin bangarori.

Adli Mansur ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar jami'a mai kula da siyasar wajen tarayyar turai Katrine Ashton, inda ya jadda cewa gwamnatin rikon kwaryar kasar ba ta niyyar mayar da wani bangare saniyar ware a cikin harkokin siyasar kasar, amma kuma a lokaci guda ba za ta yarda da ayyukan ta'addanci da sunan bayyana ra'ayi ba.

A nata bangaren Katrine Ashaton ta kirayi sabbin mahukuntan na rikon kwarya a Masar da su mayar da hankali wajen mayar da mulki ga zababbiyar gwamnati wadda za ta hada dukkanin bangarori da suka hada hard a kungiyar 'yan uwa musulmi. A nasu bangaren 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi sun yi kira ga magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatrsu gobe, domin nuna rashin amincewa da hambarar da Morsi, tare da neman a dawo das hi kan kujerar shugabancin kasar.

1266074





captcha