IQNA

Akwai Bukatar Hadin Kan Musulmi Domin Tantance Makircin Makiya

16:55 - January 07, 2015
Lambar Labari: 2684275
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Bashir Najafi babban malami daga manyan malamai na kasar Iraki ya bayyana cewa dole sai musulmi sun hada kansu ne za su iya gano makircin da makiyansu suke kulla musu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin bayanin da aike zuwa ga taron makon hadin kai Ayatollah Bashir Najafi babban malami daga manyan malamai na kasar Iraki ya bayyana cewa a halin da ake cikin yanzu dole ne sai musulmi na duniya sun hada kansu ne za su iya gano makircin da makiyansu suke kulla musu domin rarraba kansu.
Babban malamin yay i ishara da cewa al’ummar musulmi suna rayuwa cikin wani irin yanayi na daban wanda ke bukatar su zama cikin fadaka domin fayyace hakikain abin da ake kulla musu domin rarraba su da sunan addini ko banbancin mazhabobi da sauransu, wanda kuma hakan yana bukatar da yin taka tsantsan matuka wajen daukar mataki.
Sau da yawa dai malamai suna yin kira zuwa ga hadin kai tsakanin al’ummar musulmi, musamman ma dai malaman mabiya amzhabar iyalan gidan manzo, amma a wannan lokacin wadannan kiraye-kiraye suna ta kara yawa, sakamakon abin da yak faruwa a duniya na ta’addanci da sunan musulmi.
Wasu daga cikin kasashen musulmin ne abin takaici suke daukar nauyin ta’addanci da sunan addinin musulunci a cikin kasashen musulmi da ma wasu kasashen duniya, wanda hakan yak e bata sunan muslunci a idon duniya.
A safiyar yau ne dai aka bude wannan taro na hadin kan al’ummar musulmi a nan birnin Tehran wanda zai dauki kwanaki uku ana yinsa, wanda kuma ya sami halartar malamai da masana daga kimanin kasashe hamsin na musulmi.

2683089

Abubuwan Da Ya Shafa: Najafi
captcha