IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Yi Allawadai Da Zanen Batunci Da Ga Manzon Alah (SAW) A Faransa

22:10 - January 14, 2015
Lambar Labari: 2709753
Bangaren kasa da kasa, kungiyar raya al’adun musulunci ta ISESCO ta yi kakkausar suka dangane da sake yada zanen batuncin nan da jaridar Lomond ta yi ga manzon Allah (SAW) a kasar ta Faransa a yau Laraba.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, kungiyar ta yi kakkausar suka dangane da sake yada zanen batuncin nan da jaridar Lomond ta yi ga manzon Allah (SAW) a kasar ta Faransa a yau duk kuwa da irin nuna bacin rai da musulmi suka nuna dangane da abin da jaridar take yi.
Ita ma anata bangaren gwamnatin Jamhuriyar Musulunci  ta yi Allah wadai da sake buga hoton zane na batanci ga masulunci wanda jiridar nan ta Charlie Hebdo ta kasar faransa ta yi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ce ta yi wannan wadai ta kuma kara da cewa yin zanin mai batanci ga musulmi fiye da billion guda a duk fadin duniya abune wanda bai dace ba.
Kuma hakan ba abinda zai kawo in banda kara ingiza ayyukan ta’addanci a duniya, hakan nan cibiyar muslunci a masar ma ta fitar da irin wannan sanarwan inda yay i suka dangane da sake buga wannan zanen, sannan ta bayyana cewa hakan ba abinda zai haifar sai karin tashe tashen hankula a cikin mutane.
A safiyar yau ne aka saida kofi miyoyon guda na wannan jaridar kuma za’a sake buga wasu karin miliyon biyar nan gaba, dukkanin al’ummar musulmi suna ci gaba da nuna damuwa da bacin rai kan wannan lamari, tare da bayyana hakan da cewa tamkar mataki ne na tsokana ga musulmi, kuma jaridar da mahukuntan kasar ne suke da alhakin abin ya faru.

2706220

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha