IQNA

Hare-Hare Da Cin Zarafi kan Musulmi na Karuwa A Kasar Faransa

16:50 - January 20, 2015
Lambar Labari: 2736738
Bangaren kasa da kasa, masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar Faransa na ta kara tsananta harinsu da cin zarafin musulmin kasar a cikin kasa da makonni biyu tun bayan zanen batuncin da jaridar Charlir Hebdo ta yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadulo Agency cewa, yanzu haka masu tsananin kiyayya da addinin muslunci a kasar Faransa na ta kara tsananta harinsu da cin zarafin musulmin kasar a cikin kasa inda ya kai har sau 116 a cikin mako biyu.
A kasar Faransa musulmi na ci gaba da fuskantar nuna kama daga masu tsattsauran ra’ayin kin jinin addinin Musulunci. Mujallar Lopvan ta mako-mako da ake bugawa a kasar ta Faransa ta ce; A cikin wannan shekarar ta dubu biyu da sha biyar nuna kin jinin musulmi a cikin kasar ta Faransa ya rubanya har sau biyu idan aka kwatantashi da shekarar da ta gabata. 
Mujallar ta ce daga ranar bakwai  ga watan Janairu zuwa 9 a gare shi da aka kai wa mujallar Charili Hebdo hari, cutar da musulmin da aka yi a cikin wannan kasa ya rubanya. Cibiyar da ta ke fada da nunawa musulmi kama a faransa  a cikin watan janairu kadai ta iya kididdiga hare-hare da barazanar kisa da aka kai wa cibiyoyin musulmi da kuma su kansu musulmin har sau 116.
Shugaban Cibiyar mai fada da nuna kin jinin Musulunci a Faransa Abdullah ya ce; Wannan wani irin yanayi mai wuya da aka jefa musulmi a cikinsa, saboda haka ya yi kira ga gwmanatin kasar ta Faransa da ta dauki mataki da gaske domin fada da shi.
Mafi rinjayen musulmin kasar Faransa dai sun yi Allah wadai da harin da aka kai wa jaridar Charlie Hebdo, sai dai duk da haka ba su tsira ba daga fuskantar barazana da kai wa cibiyoyoyinsu na taruka da ibada hare-hare.
2734341

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha