IQNA

Kimanin 44 Ne Suka Rasa Rayukansu A Hare-Haren ta’addanci A Nigeria

17:48 - July 06, 2015
Lambar Labari: 3324171
Bnagaren kasa kasa, kimanin mutane 44 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-haren ta’addanci da aka kai jiya kan wurin cin abinci da musulmi suke buda baki yayin da wasu kimanin 67 suka samu raunuka.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Deccan Herald cewa, mutane 44 ne suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata a daren jiya Lahadi  sakamakon tashin wasu tagwayen bama-bami a birnin Jos na jahar Palteau Najeriya.

Abdulsalam Muhammad jami’I a hukumar bayar da gajin farko a kasar ya ce bam na farko ya tashi ne a wani gidan cin abinci da ke titin Bauchi a garin na Jos, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ashirin da uku tare da jikkata wasu 67.

Kafin daga bisani kuma wani bam din ya tashi a masallacin ‘yan taya, bayan yin wasu harbe-habe da bindiga a lokacin da shugaban majalisar malamai na kungiyar izala yake gabatar da tafsirin kur’ani mai tsarki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 a nan take, amma rahotanni sun ce daga bisani adadin ya karu zuwa ashirin da daya.

A nata bangaren hukumar bayar da gajin gaggawa ta Najeriya a hukumance ta ce ta ce akalla mutane 67 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren, kuma ana kula da su a asibiti, duk kuwa da cewa wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Wannan hari dai yana ci gaba da fuskantar kakakusar suka da Allawadai daga sassa daban-daban na Najeriya da ma wasu daga cikin kasashen duniya, tare da bayyana hakana matsayin wani na ta’addanci da kuma dabbanci.

3324122

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha