IQNA

Kamfe Mai Taken Whi Islama? A Jahohi 14 Na Kasar Amurka

23:25 - July 12, 2015
Lambar Labari: 3327267
Bangaren kasa da kasa, Iowa na daya daga cikin jahohi 14 na kasar Amurka da aka fara gudanar da wani kamfe mai taken why Islam? da nufin rage kaifin gabar da ake nuna ma muslunci a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga radio Iowa cewa Jawad Ahmad shi ne mai kula da kamfen da aka fara a jahar na Why Islam? da nufin  amsa tambayoyin jama’a da suke bukatar kara sani wani abu dangane da addinin muslunci.

Ahmad ya ce sun yi la’akari da cewa akwai aiki mai yawa da za su iya yi wanda zai taimaka ta fuskoki da dama domin wayar da kan Amurkawa kan addinin muslunci, da hakan ya hada da yin amfani da hanyoyi na sadarwa, daga ciki kuwa har da wannan haya.

Ya ci gaba da cewa akasarin mutane kasar Amurka ba su san addinin muslunci ba, a kan haka aka samar da shafin whyislam.org domin abin da ake gaya musu a kansa ya yi musu mummunan tasiri, a kan haka ya zama wajibi a kan su musulmin su dauki dukkanin matakan da suka dace na wayar da kai.

A cewarsa wannan day ace daga cikin hanyoyi9n da suka kirkiro domin wayar da kan muslmi, kamar yadda kuma a wasu wuraren mabiya addinin muslunci suna yin iyakacin kokarinsu domin bayyana wa Amurka cewa addinin manzon Allah addini ne na sulhu da zaman lafiya.

Bisa ga tasirin da hakan zai, sai ya ce ko shakka babu zai babban tasiri wajen kara fito da hakinanin fuskar muslunci ta zaman lafiya da fahamitar juna da giremama dan adama da rahama irin tasa ga bil adama baki daya, sabanin fahimtarsu.

Yanzu haka dai mabiya addinin mulsunci kimanin miliyan 7 da suka rayuwa  acikin kasar Amurka, wasu daga cikinsu suna zaune a wannan jaha, wasu a wasu yankunan kasar.

3326923

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha