IQNA

Ana Tilasta wa Musulmin Afirka Ta Tsakiya Domin Su Canja Addini

20:19 - August 01, 2015
Lambar Labari: 3337642
Bangaren kasa da kasa, saboda hare-haren ta’addanci kan muslmin Afirka ta tsakiya da ‘yan bindiga na Anti-Balaka ke kaiwa kansu suna tserewa zuwa wasu kasashe lamarin kan tilasta su a wasu lokuta domin barin addininsu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Dunya Blteni cewa, kungiyar Amnesty International ta sanar da cewa, mabiya addinin muslunci suna fuskantar barazana a wasu yankunan Jamhuriyar Afirka ta tsakiya daga wasu kungiyoyi na masu dauke da makamai.

Bayanin ya ce barazanar da mabiya addinin muslunci suke fuskata ce ta sanya da dama daga cikinsu ba su koma gidajensu ba da ke yankunan yammacin kasar, wanda a cewar bayanin kungiyar hakan lamari ne mai matukar hadari, wanda ya kamata bangarori na kasa da kasa su hada kai da mahukunta a kasar domin kawo karshen wannan matsala baki daya.

 

Musulmi da dama ne suka tsere suka bar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, tun bayan da rikici ya barke a cikin shekara ta dubu biyu da sha uku inda ‘yan bindiga na Anti Balaka suka yi musu kisan gilla, tare da wawushe dukiyoyinsu, tare da rushe masallatai fiye da 400 lamarin da ya sanya wasu barin kasar zuwa makwabta, yayin da wadanda ba ‘yan asalin kasar ba ne da dama daga cikinsu suka koma kasashensu.

3337263

Abubuwan Da Ya Shafa: afirka
captcha