IQNA

Ministocin Harkokin Wajen Larabawa Na Gudanar Da Zama Ya Kan Masallacin Aqsa

23:42 - August 05, 2015
Lambar Labari: 3339490
Bangaren kasa da kasa, ministocin harkokin wajen kasashen larabawa na gudanar da zama yau domin tattauna halin da ake cikin kan batun masallacin Aqsa da kuma hare-haren yahudawa.


Kamfanin dilloancin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a yau ministocin harkokin wajen kasashen larabawa na gudanar da zama na musamman domin duba halin da ake cikin kan batun masallacin Aqsa da kuma sauran batutuwa da suka shafi yankin karkashin jagorancin Sameh Shokri ministan harkokin wajen Masar.

Tarek Adel wakilin dindin na kasar Masar a kungiyar hadin kan kasashen larabawa ya bayyana cewa, ana gudanar da wannan zama na gaggawa ne tare da halartar Mahmud Abbas shugaban palastinawa, da nufin duba halin da ake da kuma sanin matakai nag aba, kan shishigin da sahyuniyawa ske kan mallacin aqsa mai alfarma  acikin kwanakin, da kuma zarafin al’ummar palasinawa.

Ya kara da cewa kasarsa na tntubar bangaren palastinu domin samun bayanai dangane da halin da ake ciki, domin samun hadin baki tsaknin dkkanin kasashen larabawa kan batun na palastine.

Ministocin harkokin na kasashen larabawa 15 ne suke halartar zaman taron, gami da kasar ta Masar wadda it ace ke rike da ragamar jagorancin kungiyar na wucin gadi.

3339291

Abubuwan Da Ya Shafa: arab League
captcha