IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Rusa Wuraren tarihi Da Daesh Ke Yi

22:44 - August 27, 2015
Lambar Labari: 3353180
Bangaren kasa da akasa, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya yi Allawadai da rusa wuraren tarihi na addinai da al’adu a cikin kasashen Syria da Iraki da yan ta’adan Daesh ke yi a wadannan kasashe.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Ina cewa, Iyad Madani  babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya yi Allawadai da rusa wuraren tarihi na addinai da al’adu a cikin kasashen Syria a wuraren Ba’al Shamin da ke cikin Tadmur da yan ta’adan Daesh ke yi a wadannan kasashe wanda hakan yay i hannun riga da dkkanin koyarwa ta kowane addini.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’ish, ta kwace iko da garin palmyra mai tarihi a kasar Syria, kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kutsa cikin birni da ke tsakiyar kasar Syria, bayan da sojojin su ka janye daga cikinsa.

Cibiyar kare hakkin bil’adama na kasar Syria, ta bakin shugabansa ya bayyana cewa; Kungiyar Is ta mamaye kusan dukkanin birnin sai dai ba ta shiga yankin da kurkuku da kuma hukumar leken asirin soja su ke ba a yammacin birnin saboda akwai sojoji masu a cikinsu.

Wanann wuri ya kasance daya daga cikin tsofaffin daulolin da aka yi  gabanin haihuwar annabi Isa da daruruwan shekaru wacce kuma ta yi  gogayya da saular roma.

Gwamnatin kasar Syria ta ce ‘yan ta’adan IS sun kashe mutane da dama a tsohon birnin tadmur dake tsakiyar kasar, bayanai sun nuna cewa akalla fararen hula dari hudu ‘yan ta’adan suka kashe a birnin na Palmyra, da suka hada  da mata da yara, bisa dalilin goyon bayan su ga shugaba kasar, da kin karbar umurni daga kungiyar ta IS a (Ba’al Shamin).

Cikin wadanda suka rasa rayukan su akwai ma'aikatan hukumomi, da na kamfanonin gwamnatin, kana akwai mutane fiye da dubu daya, wadanda kungiyar ta hana fito daga birnin mai tarihi.

3353116

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha