IQNA

Malaman Afirak sun jaddada wajabcin yaki Da Tatsauran Ra’ayin wahabiyanci

23:49 - August 29, 2015
Lambar Labari: 3353838
Bangaren kasa da kasa, fiye da malamai 300 ne suka gudanar da wani taro daga kasashen Somalia Kenya Tanzania da kuma Ethiopia gami da jamhuriyar dimokradiyyar Cono inda suka nisanta kansu daga kungiyar Alshabab.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Standard Media cewa, malaman na kasashen Afika sun nuna rashin gamsuwarsu da salon da ‘yan tra’adda suke amfani da shi domin bata sunan musulunci.

Wadannan malamai fiye da dari uku da suka gudanar da taro daga kasashen daban-daban, bayan nisanta kansu daga kungiyar ta’addanci, sun kuma kirayi dukaknin muslumi na kasashensu da su yi hakan.

A cikin yan shekarun nan dai kasashen yankin gabacin Afirka suna fuskantar gagarumar matsala ta tsaro daga kungiyoyin yan ta’adda da suke da alaka da kungiyar alkaida, wadanda suke kai hare-hare kan fararen hula.

Malaman sun ce babban burin dai shi ne isar da sakon zaman lafiya da sulhu irin na addinin muslunci, maimakon bayyana wannan adini a matsayin nay an tashin hankali da rashin son zaman lafiya kamar yadda wasu suka dauka bisa ga abin da ake gaya musu na karya da bata.

Daya daga cikin malam ya ci gaba da cewa abin da yan ta’adda suke yi da sunan muslunci ko kadan bai dace ba da koyar addinin muslunci, wanda adini ne na zamn lafiya da sulhu da kuma fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai na duniya.

3353455

Abubuwan Da Ya Shafa: Gabas
captcha