IQNA

Za A Nuna Wani Dadden Kur’ani Mai shekaru 500 A Wani Baje Koli A Madinah Munawwarah

23:33 - August 30, 2015
Lambar Labari: 3354280
Bangaren kasa da kasa, za a nuna wani dadadden kwafin kur’ani mai tsarki na tsawon karni 5 a wani baje koli kur’ani a birnin Madinah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News cewa, cibiyar sarki Abdullah Bin Abdulaziz zata dauki nauyin nuna wani dadadden kwafin kur’ani mai tsarki na tsawon shekaru 500 a wani baje koli kur’ani a birnin Madinah da a za a gudanar a cikin wannan wata.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann kur’ani yana daga cikin kur’anai dadadu da za a nuna a wannan wuri, kasantwar baje kolin zai kunshi wasu kwafin kur’anin na daban da suka hada bangarorin da aka samu wadanda a ka rbuta tun farkon bayyana musulunci.

Baya ga wannan kr’ani mai tsarki, akwai wasu kwafin kur’anan na daban da za su kasance daga cikin wannan baje koli wanda za a gudanar da shi kofa bude ga kowa duik mai son gani.

Daga ciki kuwa har da hadisan manzo da aka samu rubutunsu a kan duwatsu ko fatun dabbobi da itace da sauransu, wanda hakan zai zama mai jan hankali matuka ga masu son sanbin wani abu dangane da tarihin addinin muslunci da kuma manzo (SAW) da aka samu.

Wannan baje koli dai zai kunshi wasu hotuna na wurare masu tsarki da suke kasar da ske komawa zuwa ga tarihin addini, wadanda masana tarihi suka tabbatar da ingancinsu, da dai sauran abubuwan da ske da alaka da hakan.

3353938

Abubuwan Da Ya Shafa: Madinah
captcha