IQNA

Darul Ifta A Iraki Sun Yi Allawadai Da Shigar Turkiya A Kasarsu

20:46 - December 10, 2015
Lambar Labari: 3461989
Bangaren kasa da kasa, kungiyar malaman Ahlu sunna a kasar Iraki ta yi Allawadai da kakausar murya dangane da shigar da sojoji da Turkiya ta yi a kasarsu tare da kiran gwamnati da ta dauki mataki kan hakan.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, babbar kungiyar malaman Ahlu sunna a kasar Iraki ta yi Allawadai da kakausar murya dangane da shigar da sojoji da Turkiya ta yi zuwa Mausil da ke kasarsu tare da kiran gwamnatin Iraki da ta yi abin da ya dace.



Shieikh Khalil Alkisbi  ya ce ya zama wajibi a ladabtar da Turkiya kan hakan, yayin da gwamnatin Iraki ta sanar da cewa za ta kai karar gwamnatin Turkiya a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, dangane da batun satar danyen man fetur na kasar da ‘yan ta’addan ISIS suke yi suna shigar da shi cikin kasar Turkiya.



Shi ma Sheikh Mahdi Alsumaidai ya jaddada kiransa na cewa a kawo karshen mamayar Turkiya a cikin kasarsu kamar yadda su ma Sheikh Sa’ad Mush’an, da Hussain Fulaij Al-zauba’I duk sun bayyana irin wannan matsaya  ta neman daukar mataki kan hakan.



Gwamnatin Iraki ta sanar da hakan a ne a hukumance, inda ta jaddada cewa abin da Turkiya take yi ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, baya ga mara baya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke gudanar da ayyukan ta’adanci a Iraki da Turkiya tana sayen albarkatu na arziki da Allah ya huwace wadannan kasashe wadanda ‘yan ta’addan ISIS ke sacewa, wanda hakn a cewar bayanin gwamnatin Iraki Turkiya ta cancanci a ladabatr da ita ta hanyar doka.



A cikin ‘yan kwanakin nan jiragen yakin Rasha sun tawatsa daruruwan motocin daukar mai a kan iyakokin Syria da Turkiya, wanda ‘yan ta’addan ISIS suke amfani da su wajen shigar da mai da suke sacewa a Syria zuwa kasar Turkiya, inda Rasha ta sanar da cewa tana dalilai da ke tababtar mata da cewa shugaban Turkiya Rajab Tayyib Erdogan da wasu daga cikin iyalansa suna da hannu kai tsaye wajen hada-hadar sace man fetur na kasashen Iraki da Syria wanda ‘yan ta’addan ISIS ke yi.



3461899

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha