IQNA

Cibiyar Azhar Ta Yi Na’am Da Matakin Amincewa Da Palastinu Da Girka Ta Dauka

22:13 - December 23, 2015
Lambar Labari: 3468882
Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar Azhar ta muslunci da ke Masar ta yi na’ama da matakin da majalisar dokokin kasar Girka ta dauka na amincewa da kasar Palastinu.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na Ina cewa, a yau cibiyar Azhar ta muslunci da ke kasar Masar ta yi na’ama da matakin da majalisar dokokin kasar Girka ta dauka na amincewa da kasar Palastinu mai cin gishin kanta.

Bayanin wanda cibiyar ta fitar tare da sa hannun manyan malamanta, ya bayyana cewa wannan mataki lamari mai kyau matuka, domin ko ba komai ya kara tabbtar da cewa al’ummar palastinu suna da hakkin s zama kasa kamar kowace kasa ta duniya.

Matakin na kasar Girka dai ya zo bayan zaman da majalisar dokokin kasar ta gudanar, inda aka kada kuri’a, kma mafi yawan yan majalisar duka amince da kasar palastinu mai cin gishin kanta da ba ta karkashin yahudawa.

Girka ta bayyana wannan mataki nata da cewa ya zo ne domin bin sahihin tafarki na dimokradiya, kuma wannan shi ne matsayar al’ummar kasar, domin dukkanin yan majalisa suna wakiltar al’ummar kasar Girka ne baki daya.

Tun kafin wannan lokacin wasu daga cikin kasashe sun dauki irin wannan mataki, da suka hada har da wasu daga cikin kasashen trai, duk kuwa da cewa hakan bai yi wa haramtacciyar kasar yahudawan dadi ba.

A yayin zaman majalisar shugaban palastinawa Mahmud Abbas tare da firayi minstansa da kuma na kasar ta Girka suna tare  cikin majalisar dokokin.

3468774

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha