IQNA

Malaman Bahrain Sun Yi Suka Kan Takura Wa Al’ummar Kasar

16:53 - February 25, 2016
Lambar Labari: 3480176
Bangaren kasa da kasa, malaman addinin muslunci a kaar Bahrain sun yi kaakusar suka dangane da yadda mahkuntan kasar suke daukar matakan takura ma jama’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manama Post cewa, bayan furucin Sheikh Rashid Bin Abdollah bin Al Khalifa ministan cikin gida, gungun malaman addinin muslunci a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka kan zaluncin mahukuntan kasar da takura ma mutanen ba gaira ba sabar.

Bayanin malaman ya ce iroin matakan da ministan yake dauka matakai ne za,unci da danne hakkokin mafi yawa daga al’ummar kasar, wanda kuma hakan baya nuna komai illa kama karya.

Masarautar Bahrain ta fara daukar matakan murkuhe jama’;a da karfin tuwo tun bayan da suka fara neman hakkokinsu na siyasa a matsayinsu na yan kasa a cikin kimanin shekaru biyar da suka gabata.

A cikin wadannan shekaru an kasha daruruwan mutane da suka hada da mata da kanan yara marassa kariya, kamar yadda kuma aka daure wasu da dama a gidajen kaso ana azabtar da su.

Babban abin da ya fi bayar da mamaki kan wannan lamari dais hi ne, yadda kasashen yammacin turai masu karyar kare hakkin bil adama akasashen duniya suka yi gum da bakunansu kana bin da yake faruwa, maimakon hakan ma suna goyon bayan wannan ta’addancia siyasance tare da bayar da makamai ga wadannan azzalumai.

3478248

captcha