IQNA

Jagora Juyin Islama:

‘Yan Kasuwa A Switzerland Za Su Iya Fadada Harkokin kasuwancinsu A Iran

16:53 - February 28, 2016
Lambar Labari: 3480186
Bangaren siyasa, Ayatollah Khamenei jagoran huyi juya hali a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Switzerland ya bayyana cewa, yan kasuwa a kasar za su iya fadada harkokin kasuwancinsu a Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizi na ofishin jagora cewa, a yammacin Asabar ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaban kasar Swiss Johann Schneider-Ammann da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan Tehran inda yayin da yake ishara da tsohuwar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Jagoran ya bukaci da a kara karfafa alaka da aiki tare a fagagen tattalin arziki da ilimi a tsakaninsu yana mai cewa: Mizanin kasuwanci da saye da sayarwar da ke tsakanin Iran da Swiss yayi kadan ainun, don haka zuba jarin ‘yan kasuwar Swiss a Iran wani lamari ne da zai karfafa irin wannan alakar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin mu'amala mai kyau da Swiss ta yi da Iran a lokacin da aka sanya wa kasar takunkumi a matsayin wani fage mai kyau da zai taimaka wajen kara irin alaka da aike tare da ke tsakanin kasashen biyu, don haka sai ya ce: Mu dai tun da jimawa muna daukar kasar Swiss a matsayin wata cibiya ta sulhu, abokantaka da kuma aiki tare, duk kuwa da cewa wasu kasashen Turai din ba haka suka kasance ba. Sun mai da haifar da yaki da hair da rikici da sabani a matsayin hanyar cimma manufofinsu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin cutarwar da al'ummar Iran suka fuskanta daga siyasar neman fada da haifar da yaki na wasu kasashen Turai cikin kuwa har da irin yadda suka taimakawa tsohuwar gwamnatin Saddam Husain da makamai da jiragen yaki yayin kallafaffen yakin da ya kallafawa Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Hakan wani lamari ne da ya haifar da wani irin mummunan kallon da al'ummar Iran suke yi wa wadannan kasashen, to amma babu irin wannan kallon a kan kasar Swiss.

Har ila yau kuma yayin da yake tabbatar da lamuni kan yarjejeniya ta tattalin arziki da za a cimma tsakanin Iran da Swiss, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Abin da ke da muhimmanci shi ne a yi kokari wajen aiwatar da dukkanin yarjejeniyoyin da aka cimma a aikace.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Swiss din Johann Schneider-Ammann, wanda shugaban kasar Iran, Dakta Hasan Ruhani ke wa jagoranci ya bayyana farin cikinsa da wanan ziyarar da ya kawo Iran yana mai ishara da tsohuwar alaka da kawancen da ke tsakanin kasashen biyu. Shugaba Johann Schneider-Ammann ya ci gaba da cewa: Abin alfahari ne a gare mu irin yadda muke ganin ana samun ci gaba a alakar da ke tsakanin wadannan kasashe biyun.

Shugaban kasar ta Swiss ya ci gaba da cewa: A yayin wannan ziyarar mun tattaunawa dangane da taswirar hanyar karfafa alaka tsakanin Swiss da Iran a bangarori daban-daban, sannan kuma sanya hannu kan wannan taswirar hanya zai taimaka wajen kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin kalubalen da duniya take fuskanta a halin yanzu, shugaba Johann Schneider-Ammann ya ce: irin wannan rashin tabbas da duniya ta shiga ciki yana cutar da Turai, wanda akwai bukatar aiki tare wajen maganin wadannan matsaloli da kalubalen.

3478804

captcha